Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 7 · Aya ta 46

Al-A'raaf 7:46

الأعراف

وَبَيْنَهُمَا حِجَابٌ ۚ وَعَلَى ٱلْأَعْرَافِ رِجَالٌ يَعْرِفُونَ كُلًّۢا بِسِيمَىٰهُمْ ۚ وَنَادَوْا۟ أَصْحَـٰبَ ٱلْجَنَّةِ أَن سَلَـٰمٌ عَلَيْكُمْ ۚ لَمْ يَدْخُلُوهَا وَهُمْ يَطْمَعُونَ

Ma’ana

Kuma a tsakãninsu akwai wani shãmaki,[1] kuma a kan A'arãf akwai wasu maza sunã sanin kõwa da alãmarsu; Kuma suka kirãyi abõkan Aljamia cẽwa: "Aminci ya tabbata a kanku: "Ba su shige ta ba, alhãli kuwa sũ, sunã tsammãni.

[1] A tsakanin Aljanna da wuta akwai bango, anã ce masa A'araf, inda zã a ajiye mutãnen da ayyukansu na ƙwarai suka yi daidai da miyãgun ayyukansu. Sunã ganin mutãnen Aljanna sunã yi musu sallama sunã gurin shigarta, kuma sunã ganin mutãnen wuta sunã la'anar su, sunã neman nisanta daga gare ta.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-A'raaf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net