Al-A'raaf 7:204
الأعرافوَإِذَا قُرِئَ ٱلْقُرْءَانُ فَٱسْتَمِعُوا۟ لَهُۥ وَأَنصِتُوا۟ لَعَلَّكُمْ تُرْحَمُونَ
Kuma idan an karanta[1] Alƙur'ãni sai ku saurara gare shi, kuma ku yi shiru; Tsammãninku, anã yi muku rahama.
[1] Bãyãn an sifanta Alƙur'ãni da cewa abin kula ne ga mãsu ĩmãni, sai kuma ya yi umurni da saurãre, a lõkacin da ake karatunsa. Sauraren yana wajabta a cikin salla, idan lĩman ya bayyana karãtu kuma da a cikin huɗubar Jumma'a. Yanã zama mustahabbi ga sauran lõkatai. Kur'ãni shi ne abin da ake wa'azi da shi kuma shi ne ãyã da kansa. Hana saurãrensa yãƙi ne da gaskiya.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net