Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 7 · Aya ta 187

Al-A'raaf 7:187

الأعراف

يَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَىٰهَا ۖ قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِندَ رَبِّى ۖ لَا يُجَلِّيهَا لِوَقْتِهَآ إِلَّا هُوَ ۚ ثَقُلَتْ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ لَا تَأْتِيكُمْ إِلَّا بَغْتَةً ۗ يَسْـَٔلُونَكَ كَأَنَّكَ حَفِىٌّ عَنْهَا ۖ قُلْ إِنَّمَا عِلْمُهَا عِندَ ٱللَّهِ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ

Ma’ana

Sunã tambayar ka[1] daga Sa'a, a yaushe tabbatarta take? Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Bãbu mai bayyana ta ga lõkacinta fãce shĩ Tã yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Bã zã ta zo muku ba fãce kwatsam." sunã tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawan mutãne bã su sani."

[1] Tambayar abin da Allah bai bayyana shi ba, kamar Rãnar Tãshin Kiyãma, yãƙi ne a tsakanin ƙarya da gaskiya. cewa wani mutum yã san gaibi ko yanã iya kãwo alheri kõ ya tunkuɗe wani sharri, ƙarya ne, kuma faɗã da gaskiya ne.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-A'raaf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net