Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 7 · Aya ta 180

Al-A'raaf 7:180

الأعراف

وَلِلَّهِ ٱلْأَسْمَآءُ ٱلْحُسْنَىٰ فَٱدْعُوهُ بِهَا ۖ وَذَرُوا۟ ٱلَّذِينَ يُلْحِدُونَ فِىٓ أَسْمَـٰٓئِهِۦ ۚ سَيُجْزَوْنَ مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ

Ma’ana

Kuma Allah Yanã da sũnãye mãsu kyau.[1] Sai ku rõƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhãdi a cikin sũnãyenSa: zã a sãka musu abin da suka kasance sunã aikatãwa.

[1] Waɗanda suke rõƙon Allah bã da sũnãyenSa mãsu kyau ba, sũ ne aka sifanta da dabbõbi, har dabbõbi sun fi su, dõmin dabba tanã gudun abinda yake cũtar ta, amma sũ ba su san abin da yake cũtar su ba, balle su guje shi. Kuma anã fahimtar cewa bã a rõƙon Allah da wani sũna Nãsa, idan bai kasance a cikin sanayenSa mãsu kyau ba, sai fa idan ya zama a dunƙule ne, kamar a ce, "Ya Allah inã rõƙonKa da sũnayenKa waɗanda na sani da waɗanda ban sani ba," dõmin Hadĩsi ya nũna a yi haka. Kiran Allah bã da sunãyenSa mãsu kyau ba yana cikin yãƙi a tsakãnin ƙarya da gaskiya.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-A'raaf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net