Al-A'raaf 7:175
الأعرافوَٱتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ ٱلَّذِىٓ ءَاتَيْنَـٰهُ ءَايَـٰتِنَا فَٱنسَلَخَ مِنْهَا فَأَتْبَعَهُ ٱلشَّيْطَـٰنُ فَكَانَ مِنَ ٱلْغَاوِينَ
Ka karanta a kansu lãbãrin wanda Muka kãwo masa[1] ãyõyinMu, sai ya sãɓule daga gare su, sai shaidan ya bi shi, sai ya kasance a cikin halakakku.
[1] Asalin ƙissar anã cewa daga Bil'amu ɗan Bã'ura ne; Allah ya bã shi ilmi, sai ya bar ilmin. Yanã daga cikin mãlaman Banĩ Isrã' ĩla, yã kasance wanda ake karɓar addu'arsa, sunã gabatar da shi a cikin tsanance-tsanance, sai Mũsã ya aike shi zuwa ga sarkin Madyana ya kirãye shi zuwa ga Allah. Sai sarkin ya yanka masa ƙasa, ya bã shi, sai ya bi addinin sarkin, ya bar addinin Mũsã. Ya zama misãli ga duk mãlamin da bai yi aiki da ilminsa ba. Idan mãlami ya halaka, to, yã fi Shaiɗan sharri dõmin haka shaiɗan yake binsa wajen taimakon ƙarya a kan gaskiya.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net