Al-A'raaf 7:171
الأعرافوَإِذْ نَتَقْنَا ٱلْجَبَلَ فَوْقَهُمْ كَأَنَّهُۥ ظُلَّةٌ وَظَنُّوٓا۟ أَنَّهُۥ وَاقِعٌۢ بِهِمْ خُذُوا۟ مَآ ءَاتَيْنَـٰكُم بِقُوَّةٍ وَٱذْكُرُوا۟ مَا فِيهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ
Kuma a lõkacin da muka ɗaukaka dũtse[1] sama da su, kumar dai shi girgije ne, kuma suka haƙƙaƙe, lalle ne shĩ, mai fãɗuwa ne a gare su, (aka ce): "Ku karɓi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi, kuma ku tuna abin da yake a cikinsa, tsammãninku kunã yin taƙawa."
[1] A lõkacin da Mũsã ya karanta wa Banĩ Isra'ila Attaura da hukunce-hukuncen da suke a cikinta, mãsu wuya gare su, sai suka ƙi yarda da ita. Allah Ya yanka dũtse daidai da garinsu, Ya ɗaukaka shi a kansu, ko su yi aiki da ita kõ ya fãɗa a kansu. Daga nan idan suna salla, sai su yi sujada da rabin gõshi a kan tsãgin hagu, sunã kallon dũtsen. Kuma yin sujada a haka ya zama sunnarsu har yanzu. Watau bã a iya tsare gaskiya daga yãƙin ƙarya sai an yi amfãni da wani ƙarfi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net