Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 7 · Aya ta 169

Al-A'raaf 7:169

الأعراف

فَخَلَفَ مِنۢ بَعْدِهِمْ خَلْفٌ وَرِثُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ يَأْخُذُونَ عَرَضَ هَـٰذَا ٱلْأَدْنَىٰ وَيَقُولُونَ سَيُغْفَرُ لَنَا وَإِن يَأْتِهِمْ عَرَضٌ مِّثْلُهُۥ يَأْخُذُوهُ ۚ أَلَمْ يُؤْخَذْ عَلَيْهِم مِّيثَـٰقُ ٱلْكِتَـٰبِ أَن لَّا يَقُولُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلْحَقَّ وَدَرَسُوا۟ مَا فِيهِ ۗ وَٱلدَّارُ ٱلْـَٔاخِرَةُ خَيْرٌ لِّلَّذِينَ يَتَّقُونَ ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَ

Ma’ana

Sai wasu' yan bãya suka maye daga bãyansu, sun gaji Littãfin, sunã karɓar sifar[1] wannan ƙasƙantacciya, sunã cẽwa: "Zã a gãfarta mana. "Iadan kuma wata sifa irinta ta zo, za su karɓe ta. Shin, ba a karɓi alkawarin Littãfi ba a kansu cẽwa kada su faɗa ga Allah, fãce gaskiya, alhãli kuwa sun karanta abin da yake a cikinsa, kuma Gidan Lãhira ne mafi alhẽriga wanda ya yi taƙawa? Shin, bã zã ku hankalta ba?

[1] Sifar ƙasƙantacciya ita ce kãyan dũniya na haram, kamar rashawa. An kira ta sifa dõmin bã aba ce mai tsayuwa da kanta ba, kuma bã sifar abin kirki ba, sai dai abin da yake halaka ne nan da nan. Tãke gaskiya faɗa ne da Addini, watau yaƙi a tsakãnin gaskiya da ƙarya.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-A'raaf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net