Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 7 · Aya ta 157

Al-A'raaf 7:157

الأعراف

ٱلَّذِينَ يَتَّبِعُونَ ٱلرَّسُولَ ٱلنَّبِىَّ ٱلْأُمِّىَّ ٱلَّذِى يَجِدُونَهُۥ مَكْتُوبًا عِندَهُمْ فِى ٱلتَّوْرَىٰةِ وَٱلْإِنجِيلِ يَأْمُرُهُم بِٱلْمَعْرُوفِ وَيَنْهَىٰهُمْ عَنِ ٱلْمُنكَرِ وَيُحِلُّ لَهُمُ ٱلطَّيِّبَـٰتِ وَيُحَرِّمُ عَلَيْهِمُ ٱلْخَبَـٰٓئِثَ وَيَضَعُ عَنْهُمْ إِصْرَهُمْ وَٱلْأَغْلَـٰلَ ٱلَّتِى كَانَتْ عَلَيْهِمْ ۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ بِهِۦ وَعَزَّرُوهُ وَنَصَرُوهُ وَٱتَّبَعُوا۟ ٱلنُّورَ ٱلَّذِىٓ أُنزِلَ مَعَهُۥٓ ۙ أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُفْلِحُونَ

Ma’ana

"Waɗanda suke sunã bin Manzo[1], Annabi, Ummiyyi wanda suke sãmun sa rubũce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla.yanã umurnin su da alhẽri, kuma yana hana su daga barin abin da bã a so; kuma yana halatta musu abũ- buwa masu dadi, kuma yana haramtarwar mũnana a kansu. Kuma yanã kãyar da nauyinsu daga barinsu, da ƙuƙummai waɗannan da suka kasance a kansu. To, wa- ɗanda suka yi ĩmãni da shi kuma suka ƙarfafa shi, kuma suka tai- make shi, kuma suka bi haske wan- da aka saukar tãre da shi, waɗan- nan ne mãsu cin nasara.

[1] Bayãnin bisharar Attaura da Linjĩla game da Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gare shi. Kuma bishãrar da Allah ya gaya wa Annabi Mũsã wurin Miƙatinsa tãre da mutãne saba'in, dõmin maganar ɗinke take.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-A'raaf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net