Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 7 · Aya ta 137

Al-A'raaf 7:137

الأعراف

وَأَوْرَثْنَا ٱلْقَوْمَ ٱلَّذِينَ كَانُوا۟ يُسْتَضْعَفُونَ مَشَـٰرِقَ ٱلْأَرْضِ وَمَغَـٰرِبَهَا ٱلَّتِى بَـٰرَكْنَا فِيهَا ۖ وَتَمَّتْ كَلِمَتُ رَبِّكَ ٱلْحُسْنَىٰ عَلَىٰ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ بِمَا صَبَرُوا۟ ۖ وَدَمَّرْنَا مَا كَانَ يَصْنَعُ فِرْعَوْنُ وَقَوْمُهُۥ وَمَا كَانُوا۟ يَعْرِشُونَ

Ma’ana

Kuma Muka gãdar da mutãnen, waɗanda sun kasance anã raunana su, a gabacin ƙasa da yammacinta, wadda Muka sanya albarka a cikinta, kuma kalmar Ubangijinka mai kyau ta cika a kan Banĩ Isrã'ĩla, sabõda abin dasuka yi na haƙuri. Kuma Muka murtsuke abin da Fir'auna da mutãnensa suka kasance sunã sanã'antawa, da abin da suka kasance sunã shimfiɗãwa.[1]

[1] Wannan shi ne ƙarshen ƙissar faɗan gaskiya daga wajen Mũsã da ƙarya daga wajen Fir'auna da rundunarsa da dũkiyarsa. Haka dai ƙarya kõme duhunta, to, na banzane, a ƙarshe zã ta wãtsa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-A'raaf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net