Al-A'raaf 7:133
الأعراففَأَرْسَلْنَا عَلَيْهِمُ ٱلطُّوفَانَ وَٱلْجَرَادَ وَٱلْقُمَّلَ وَٱلضَّفَادِعَ وَٱلدَّمَ ءَايَـٰتٍ مُّفَصَّلَـٰتٍ فَٱسْتَكْبَرُوا۟ وَكَانُوا۟ قَوْمًا مُّجْرِمِينَ
Sai Muka aika a kansu da cikõwa, da fãra, da ƙwarƙwata da kwãɗi, da jini; ãyõyi abũbuwan rarrabẽwa[1]; Sai suka kangare, kuma suka kasance mutãne mãsu laifi.
[1] Ãyõyin da suka je musu a cikin lõkatai daban-daban dõmin a ja hankalinsu, kõ zã su yi ĩmãni. Kõwace ãyã tanã kwãna bakwai sunã wahala da ita, sa'an nan su rõƙi Mũsã ya yi addu'a a kuranye ta, sa'an nan a bãyan wani lõkaci sai su kõma wa kãfircinsu, kamar yadda ãyõyi mãsu biyar wannan suka bayyana.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net