Al-A'raaf 7:128
الأعرافقَالَ مُوسَىٰ لِقَوْمِهِ ٱسْتَعِينُوا۟ بِٱللَّهِ وَٱصْبِرُوٓا۟ ۖ إِنَّ ٱلْأَرْضَ لِلَّهِ يُورِثُهَا مَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦ ۖ وَٱلْعَـٰقِبَةُ لِلْمُتَّقِينَ
Mũsã ya ce wa mutãnensa:[1] "Ku nẽmi taimako da Allah, kuma ku yi haƙuri; Lalle ne ƙasa ta Allah ce, Yãna gãdar da ita ga wanda Yake so daga bãyinSa, kuma ãƙiba ta mãsu taƙawa ce."
[1] Maganar Mũsã ga Banĩ Isrã'ila tã nũna cewa sun ga azãbar ta yi musu yawa, har sun fãra zargin Mũsã da cewa ya sabbaba musu tsananin fitinar, da zõwarsa. Shi kuma ya lallãshe su da cewa, "Kõme ya yi tsanani, to, sauƙin sa ya yi kusa.".
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net