Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 7 · Aya ta 126

Al-A'raaf 7:126

الأعراف

وَمَا تَنقِمُ مِنَّآ إِلَّآ أَنْ ءَامَنَّا بِـَٔايَـٰتِ رَبِّنَا لَمَّا جَآءَتْنَا ۚ رَبَّنَآ أَفْرِغْ عَلَيْنَا صَبْرًا وَتَوَفَّنَا مُسْلِمِينَ

Ma’ana

"Kuma bã ka zargin kõme daga gare mu fãce dõmin mun yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinmu a lõkacin da suka zõ mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu, kuma Ka cika mana munã Musulmai![1] "

[1] Musulmi shi ne wanda ya sallama kansa ga hukunce-hukuncen Allah waɗanda wani Annabin Allah ya zõ da su, a cikin zãmaninsa. Sabõda haka ma'anar Musulmi shi ne mai sallamãwa ga hukuncin Allah, a kõwane zãmani, tun daga Ãdamu har zuwa Rãnar Ƙiyãma. Sai dai wannan al'umma ta Muhammadu tã keɓanta da sũnan Musulmi, addinin kuma da sũnan Musulunci.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-A'raaf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net