Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 66 · Aya ta 10

At-Tahrim 66:10

التحريم

ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلًا لِّلَّذِينَ كَفَرُوا۟ ٱمْرَأَتَ نُوحٍ وَٱمْرَأَتَ لُوطٍ ۖ كَانَتَا تَحْتَ عَبْدَيْنِ مِنْ عِبَادِنَا صَـٰلِحَيْنِ فَخَانَتَاهُمَا فَلَمْ يُغْنِيَا عَنْهُمَا مِنَ ٱللَّهِ شَيْـًٔا وَقِيلَ ٱدْخُلَا ٱلنَّارَ مَعَ ٱلدَّٰخِلِينَ

Ma’ana

Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka kãfirta[1]: mãtar Nũhu da mãtar Lũɗu, sun kasance a ƙarƙashin wasu bãyi biyu daga bãyin Mu sãlihai, sai suka yaudare su, sabõda haka ba su wadãtar musu da kõme daga Allah ba. Kuma aka ce: "Ku shiga, kũ biyu, wutã tãre da mãsu shiga."

[1] Waɗannan misãlai biyu,mãtar Nũhu da mãtar Lũɗu sunã nũna kusanci ga sãlihai bã ya isa ga addini sai kõwa ya yi abin da Allah Ya yi umurni da shi. Kuma anã kallafa wa mãtã da su kiyãye kyawun zamantakewa da mazansu. Kuma anã yi musu azãba sabõda sãɓa wa Allah ga barin haka kamar yadda ake ga mazansu.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tahrim

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net