Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 65 · Aya ta 8

At-Talaaq 65:8

الطلاق

وَكَأَيِّن مِّن قَرْيَةٍ عَتَتْ عَنْ أَمْرِ رَبِّهَا وَرُسُلِهِۦ فَحَاسَبْنَـٰهَا حِسَابًا شَدِيدًا وَعَذَّبْنَـٰهَا عَذَابًا نُّكْرًا

Ma’ana

Kuma da yawa[1] daga alƙarya wadda ta yi tsaurin kai daga barin umurnin Ubangijinta da ManzanninSa, sai Muka yi mata hisãbi, hisãbi mai tsanani, kuma Muka, azabtar da ita azãba abar ƙyãma.

[1] A bãyan da ya gama bayãnin saki da hukunce-hukuncen da suka rãtayu a gare shi, sai kuma ya gõya gargaɗi ga wanda bai bi waɗannan hukunce-hukuncen ba, ta hanyar tsoratar da shi da cewa Allah Ya halaka alƙaryu mãsu yawa sabõda sãɓã Masa ga hukunce-hukuncen Sa ga ƙanãnan abũbuwa, balle mutum guda wanda ya sãɓã masa ga babban al'amari kamar aure da saki waɗanda rãyuwar ɗan Adam ta dõgara a kansu kuma ya yi bushãra ga wanda ya bĩ shi da taƙawa, ya fita daga duhun al'ãdu zuwa ga hasken sharĩ'ar Sa, kuma Ya yi wa'adi da bã shi sauƙin rãyuwa daga wadãtar Sa mai yawa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Talaaq

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net