Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 65 · Aya ta 11

At-Talaaq 65:11

الطلاق

رَّسُولًا يَتْلُوا۟ عَلَيْكُمْ ءَايَـٰتِ ٱللَّهِ مُبَيِّنَـٰتٍ لِّيُخْرِجَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ مِنَ ٱلظُّلُمَـٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ ۚ وَمَن يُؤْمِنۢ بِٱللَّهِ وَيَعْمَلْ صَـٰلِحًا يُدْخِلْهُ جَنَّـٰتٍ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ خَـٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًا ۖ قَدْ أَحْسَنَ ٱللَّهُ لَهُۥ رِزْقًا

Ma’ana

Manzo, yanã karãtun ãyõyin Allah bayyananu a kanku dõmin Ya fitar da waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai daga duffai zuwa ga haske. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah ya aikata aikin ƙwarai Allah zai shigar da shi gidãjen Aljanna ƙoramu nã gudãna daga ƙarƙashinsu sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada. Haƙĩƙa Allah Yã kyautata[1] masa arziki.

[1] Allah Yã kyautata wa wanda ya tsare sharĩ'arsa da kyau, awajen arzikinsa tun daga dũniya har ya zuwa Lãhira, dõmin Yã ce: "Haƙĩƙa Allah Yã kyautatã masa (mai tsare sharĩ'ar) arziki," bã da Yã yi ƙaidin lõkaci kõ wuri ba.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Talaaq

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net