Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 63 · Aya ta 8

Al-Munaafiqoon 63:8

المنافقون

يَقُولُونَ لَئِن رَّجَعْنَآ إِلَى ٱلْمَدِينَةِ لَيُخْرِجَنَّ ٱلْأَعَزُّ مِنْهَا ٱلْأَذَلَّ ۚ وَلِلَّهِ ٱلْعِزَّةُ وَلِرَسُولِهِۦ وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَلَـٰكِنَّ ٱلْمُنَـٰفِقِينَ لَا يَعْلَمُونَ

Ma’ana

Sunã cẽwa "Lalle ne idan mun kõma[1] zuwa Madĩnar, haƙĩƙa mafi rinjaya zai fitar da mafi ƙasƙanta daga gare ta, alhãli kuwa rinjãyar ga Allah take kuma da ManzonSa, kuma da mũminai, kuma amma munãfikai ba su sani ba."

[1] Abdullah bn Ubayyi bn Salũl ya faɗi cewa "Wallahi idan mun kõma Madĩna wanda ya fi ƙarfi, lalle zai fitar da wanda ya fi ƙasƙanci." Yanã nufin Ansãrai mutãnen Madĩna zã su kõri Muhãjirai. Yã faɗi haka a cikin wata tafiya ta jihãdi. Aka gaya wa Annabi, sai ya yi musu. Allah Ya kunyata shi.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Munaafiqoon

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net