Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 60 · Aya ta 1

Al-Mumtahana 60:1

الممتحنة

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَتَّخِذُوا۟ عَدُوِّى وَعَدُوَّكُمْ أَوْلِيَآءَ تُلْقُونَ إِلَيْهِم بِٱلْمَوَدَّةِ وَقَدْ كَفَرُوا۟ بِمَا جَآءَكُم مِّنَ ٱلْحَقِّ يُخْرِجُونَ ٱلرَّسُولَ وَإِيَّاكُمْ ۙ أَن تُؤْمِنُوا۟ بِٱللَّهِ رَبِّكُمْ إِن كُنتُمْ خَرَجْتُمْ جِهَـٰدًا فِى سَبِيلِى وَٱبْتِغَآءَ مَرْضَاتِى ۚ تُسِرُّونَ إِلَيْهِم بِٱلْمَوَدَّةِ وَأَنَا۠ أَعْلَمُ بِمَآ أَخْفَيْتُمْ وَمَآ أَعْلَنتُمْ ۚ وَمَن يَفْعَلْهُ مِنكُمْ فَقَدْ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ

Ma’ana

Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku riƙi maƙiyĩ Na kuma maƙiyinku masõyi, . Kuna jẽfa sõyayya[1] zuwa gare su, alhãli kuwa haƙĩƙa sun kãfirta da abin da ya zo muku, na gaskiya, sunã fitar da Manzon Allah tãre da ku (daga gidãjenku) dõmin kun yi ĩmãni da Allah, Ubangijinku, idan kun fito dõmin jihãdi sabõda ɗaukaka kalmaTa da nẽman yardaTa, kunã asirta sõyayya zuwa gare su alhãli kuwa Nĩ ne Mafi sani ga abin da kuka ɓõye da abin da kuka bayyana, kuma duk wanda ya aikata shi daga cikinku, to, lalle ya ɓace daga tsakar hanya.

[1] Wani Sahãbin Annabi da ake cewa Hãtibu bn Abi Balta'a, ya rubũta takarda zuwa ga Ƙuraishãwa yanã sanar da su cewa Annabi na zuwa garinsu da yãƙi, sai Allah Ya sanar da Annabi tun manzonsa bai isa ba ga Ƙuraishãwa, sai aka mayar da takardar. Da aka tambayi Hãtibu dalĩlin yin ta,sai ya ce dõmin yanã da ɗiya da dũkiya ne a can, dõmin haka ya so ya gaya musu zuwan Annabi kõ da yake yanã da cikakken ĩmãmin cewa Annabi gaskiya ne, kuma zai rinjãye su duk yadda aka yi. Sai Annabi ya karɓi uzurinsa, ba a yi masa kõme ba, sai dai abin da Allah Ya hana; kada Musulmi su sãke wata ma'amala da kãfirai a ɓõye, ko a bayyane sabõda dalĩlan da aka faɗa a cikin sũrar.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Mumtahana

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net