Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 6 · Aya ta 95

Al-An'aam 6:95

الأنعام

إِنَّ ٱللَّهَ فَالِقُ ٱلْحَبِّ وَٱلنَّوَىٰ ۖ يُخْرِجُ ٱلْحَىَّ مِنَ ٱلْمَيِّتِ وَمُخْرِجُ ٱلْمَيِّتِ مِنَ ٱلْحَىِّ ۚ ذَٰلِكُمُ ٱللَّهُ ۖ فَأَنَّىٰ تُؤْفَكُونَ

Ma’ana

Lalle ne, Allah ne Mai tsãgewar ƙwãyar hatsi da kwalfar gurtsu. Yanã fitar da mai rai daga mamaci, kuma (Shi) Mai fitar da mamaci ne daga mai rai,[1] wannan ne Allah. To, yãya ake karkatar da ku?

[1] Mai ĩmãni daga kãfiri kõ kãfiri daga mai ĩmãni, da mai arziki daga matalauci da matalauci daga mawadãci, sarki daga talaka da talaka daga sarki,da mai sanyi daga mai zãfi ko mai zãfi daga mai sanyi, haka dai ga kõme Allah Yanã fitar da kĩshiyarsa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-An'aam

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net