Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 6 · Aya ta 71

Al-An'aam 6:71

الأنعام

قُلْ أَنَدْعُوا۟ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُنَا وَلَا يَضُرُّنَا وَنُرَدُّ عَلَىٰٓ أَعْقَابِنَا بَعْدَ إِذْ هَدَىٰنَا ٱللَّهُ كَٱلَّذِى ٱسْتَهْوَتْهُ ٱلشَّيَـٰطِينُ فِى ٱلْأَرْضِ حَيْرَانَ لَهُۥٓ أَصْحَـٰبٌ يَدْعُونَهُۥٓ إِلَى ٱلْهُدَى ٱئْتِنَا ۗ قُلْ إِنَّ هُدَى ٱللَّهِ هُوَ ٱلْهُدَىٰ ۖ وَأُمِرْنَا لِنُسْلِمَ لِرَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ

Ma’ana

Ka ce: "Shin, zã mu yi kiran abin da bã ya amfãninmu, baicin Allah, kuma bã ya cũtar damu, kuma a mayar da mu a kan dugãduganmu, a bayan Allah Yã shiryar da mu kamar wanda shaiɗãnu suka kãyar da shi a cikin ƙasa, yanã mai ɗĩmuwa, yanã da abõkaisunã kiran sa zuwa ga shiriya, 'Ka zo mana'"[1] Kace: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya. Kuma an umurce mu, mu sallama wa Ubangijin tãlikai."

[1] Shi kuma bã ya karɓãwa balle ya nufi wurin shiriyar da suke kiran sa ya tafi, sabõda yã riga yã fãɗi daga sama zuwa ƙasa, kuma ɗimuwa tã kãmã shi.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-An'aam

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net