Al-An'aam 6:60
الأنعاموَهُوَ ٱلَّذِى يَتَوَفَّىٰكُم بِٱلَّيْلِ وَيَعْلَمُ مَا جَرَحْتُم بِٱلنَّهَارِ ثُمَّ يَبْعَثُكُمْ فِيهِ لِيُقْضَىٰٓ أَجَلٌ مُّسَمًّى ۖ ثُمَّ إِلَيْهِ مَرْجِعُكُمْ ثُمَّ يُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
Kuma Shĩ ne wanda Yake karɓar[1] rãyukanku da dare, kuma Yanã sanin abin da kuka yãga da rãna, sa'an nan Yanã tãyar da ku a cikinsa, dõmin a hukunta ajali ambatacce sa'an nan kuma zuwa gare shi makõmarku take, sa'an nan kuma Ya ba ku lãbari da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
[1] Karɓar rai da dare dõmin barci, tãyarwa a cikin ranã, watau yini daga barci. Akwai misalta dare da dũniya kuma rãna da Rãnar Ƙiyãma, kuma mutuwa da barci, da farkawa daga barci da Tãshin Ƙiyãma. Ãyar tã ƙunsa asĩrai mãsu yawa.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net