Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 6 · Aya ta 20

Al-An'aam 6:20

الأنعام

ٱلَّذِينَ ءَاتَيْنَـٰهُمُ ٱلْكِتَـٰبَ يَعْرِفُونَهُۥ كَمَا يَعْرِفُونَ أَبْنَآءَهُمُ ۘ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ فَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ

Ma’ana

Waɗanda Muka bã su Littãfi sunã sanin sa[1] kamar yadda suke sanin ɗiyansu. Waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu, to, sũ bã su yin ĩmãni.

[1] Yahũdu da Nasãra sunã sanin Annabi Muhammadu tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, da abin da ya zo da shi na Alƙur'ãni, kamar yadda suka san ɗiyan tsatsõnsu; kamar yadda Abdullahi ɗan Sallãmi ya ce wa Umar: "Lalle ne na san shi a lõkacin da na gan shi, kamar yadda nake sanin ɗãna, kuma lalle ne, ni, mãfi tsananin sani ne ga Muhammadu fiye da ɗãna.".

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-An'aam

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net