Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 6 · Aya ta 124

Al-An'aam 6:124

الأنعام

وَإِذَا جَآءَتْهُمْ ءَايَةٌ قَالُوا۟ لَن نُّؤْمِنَ حَتَّىٰ نُؤْتَىٰ مِثْلَ مَآ أُوتِىَ رُسُلُ ٱللَّهِ ۘ ٱللَّهُ أَعْلَمُ حَيْثُ يَجْعَلُ رِسَالَتَهُۥ ۗ سَيُصِيبُ ٱلَّذِينَ أَجْرَمُوا۟ صَغَارٌ عِندَ ٱللَّهِ وَعَذَابٌ شَدِيدٌۢ بِمَا كَانُوا۟ يَمْكُرُونَ

Ma’ana

Kuma idan wata ãyã ta je musu sai su ce: "Ba zã mu yi ĩmãni ba, sai an kãwo mana kamar abin da aka kãwo wa manzannin Allah." Allah Mafi sanin inda Yake sanya manzancinSa.[1] Wani wulaƙanci[2] a wurin Allah da wata azãba mai tsanani zã su sãmi waɗanda suka yi laifi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na mãkirci.

[1] Manzanci da zãɓin Allah yake, bã da kuɗi kõ'ya'ya kõ kabĩla yake ba, sai a wurin da Allah Ya aza shi.
[2] Mai girman kai ga bin umurnin Allah, sakamakonsa wulaƙanci ne.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-An'aam

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net