Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 59 · Aya ta 9

Al-Hashr 59:9

الحشر

وَٱلَّذِينَ تَبَوَّءُو ٱلدَّارَ وَٱلْإِيمَـٰنَ مِن قَبْلِهِمْ يُحِبُّونَ مَنْ هَاجَرَ إِلَيْهِمْ وَلَا يَجِدُونَ فِى صُدُورِهِمْ حَاجَةً مِّمَّآ أُوتُوا۟ وَيُؤْثِرُونَ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمْ وَلَوْ كَانَ بِهِمْ خَصَاصَةٌ ۚ وَمَن يُوقَ شُحَّ نَفْسِهِۦ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُفْلِحُونَ

Ma’ana

Da waɗanda suka zaunar da gidãjensu (ga Musulunci) kuma (suka zãɓi) ĩmãni, a gabãnin zuwansu,[1] sunã son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma bã su tunãnin wata bukãta a cikin ƙirãzansu daga abin da aka bai wa muhãjirĩna, kuma sunã fĩfĩta waɗansu a kan kãwunansu, kuma ko dã sunã da wata larũra. Wanda ya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.

[1] Muhãjirĩna sun yi hijira zuwa Madĩna daga Makka kõ waɗansu wurãre. Ansar, su ne mutãnen Madĩna. Waɗannan sũ ne ya kamãta a yi mãmãkin yadda suka taimaki addini a lõkacin tsanani. Muhãjirina sun bar gidãjensu da dũyarsu sun yi hijira, Ansarai sun raba dũkiyarsu da gidãjensu da iyãlansu sun bai wa Muhãjirĩna dõmin taimakon addĩni.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Hashr

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net