Al-Hashr 59:11
الحشرأَلَمْ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ نَافَقُوا۟ يَقُولُونَ لِإِخْوَٰنِهِمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ مِنْ أَهْلِ ٱلْكِتَـٰبِ لَئِنْ أُخْرِجْتُمْ لَنَخْرُجَنَّ مَعَكُمْ وَلَا نُطِيعُ فِيكُمْ أَحَدًا أَبَدًا وَإِن قُوتِلْتُمْ لَنَنصُرَنَّكُمْ وَٱللَّهُ يَشْهَدُ إِنَّهُمْ لَكَـٰذِبُونَ
Ashe, ba ka ga waɗanda suka yi munãfinci[1]ba, sunã cẽwa ga 'yan'uwansu, waɗanda suka kãfirta daga Mazõwa Littafi, "Lalle idan an fitar da ku, lalle zã mu fita tãre da ku, kuma bã zã mu yi ɗã'a ga kõwa ba game da ku, har abada, kuma lalle idan an yãƙe ku, lalle zã mu taimake ku haƙĩƙatan?" Alhãli kuwa Allah na shaidar cẽwa lalle sũ tabbas, maƙaryata ne.
[1] Bãyan ya nũna yadda Allah ke taimakon mai binsa da taƙawa. Kuma yanã nũna yadda Yake tãɓar da mai binSa da munãfinci.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net