Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 58 · Aya ta 7

Al-Mujaadila 58:7

المجادلة

أَلَمْ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ ۖ مَا يَكُونُ مِن نَّجْوَىٰ ثَلَـٰثَةٍ إِلَّا هُوَ رَابِعُهُمْ وَلَا خَمْسَةٍ إِلَّا هُوَ سَادِسُهُمْ وَلَآ أَدْنَىٰ مِن ذَٰلِكَ وَلَآ أَكْثَرَ إِلَّا هُوَ مَعَهُمْ أَيْنَ مَا كَانُوا۟ ۖ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوا۟ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِكُلِّ شَىْءٍ عَلِيمٌ

Ma’ana

Ashe, ba ka ga cẽwa lalle Allah Yanã sane da abin da yake a cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa ba? Wata gãnãwa[1] ta mutum uku bã zã ta kasance ba fãce Allah Shĩ ne na huɗu ɗinta, kuma bãbu ta mutum biyar fãce Shĩ ne na shida ɗinta, kuma babu abin da ya kãsa wannan kuma babu abin da yake mafi yawa fãce Shĩ Yanã tãre da su duk inda suka kasance, sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka aikata a Rãnar ¡iyãma. Lalle Allah Masani ne ga dukkan kõme.

[1] A bãyan ƙissar zihãri, ya shiga maganar mãsu gãnãwa a cikin majalisa. Kuma ya nuna cewa ba a sifanta Annabi kõ a jingina wani abu zuwa gare shi sai idan abin nan yã fito daga Allah a cikin harshen Manzon Sa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Mujaadila

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net