Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 58 · Aya ta 12

Al-Mujaadila 58:12

المجادلة

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِذَا نَـٰجَيْتُمُ ٱلرَّسُولَ فَقَدِّمُوا۟ بَيْنَ يَدَىْ نَجْوَىٰكُمْ صَدَقَةً ۚ ذَٰلِكَ خَيْرٌ لَّكُمْ وَأَطْهَرُ ۚ فَإِن لَّمْ تَجِدُوا۟ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ

Ma’ana

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan zã ku gãnãwa da Manzon Allah, to, ku gabãtar da 'yar sadaka[1] a gabãnin gãnãwarku, wannan ne mafi alhẽri a gare ku, kuma mafi tsarki. Sai idan ba ku sãmi (abin sadakar ba), to, lalle, Allah, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

[1] Hukuncin tãyar da mutãne dõmin a gãna da Manzon Allah, bã ya halatta sai a kan larũra mai tsanani sabõda haka aka sanya gabãtar da sadaka, sa'an nan aka sõke shi da umurni da tsaron salla dõmin wa'azin da ke cikinta da kuma bayar da zakka.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Mujaadila

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net