An-Najm 53:32
النجمٱلَّذِينَ يَجْتَنِبُونَ كَبَـٰٓئِرَ ٱلْإِثْمِ وَٱلْفَوَٰحِشَ إِلَّا ٱللَّمَمَ ۚ إِنَّ رَبَّكَ وَٰسِعُ ٱلْمَغْفِرَةِ ۚ هُوَ أَعْلَمُ بِكُمْ إِذْ أَنشَأَكُم مِّنَ ٱلْأَرْضِ وَإِذْ أَنتُمْ أَجِنَّةٌ فِى بُطُونِ أُمَّهَـٰتِكُمْ ۖ فَلَا تُزَكُّوٓا۟ أَنفُسَكُمْ ۖ هُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ ٱتَّقَىٰٓ
Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake[1] kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa.
[1] Wanda yake mutumin kirki, Allah Ya san shi. Kada ku dinga tsarkake kanku da bãkunanku dõmin neman girma, kõ dõmin neman wani abu dabam.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net