Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 52 · Aya ta 21

At-Tur 52:21

الطور

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَٱتَّبَعَتْهُمْ ذُرِّيَّتُهُم بِإِيمَـٰنٍ أَلْحَقْنَا بِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَمَآ أَلَتْنَـٰهُم مِّنْ عَمَلِهِم مِّن شَىْءٍ ۚ كُلُّ ٱمْرِئٍۭ بِمَا كَسَبَ رَهِينٌ

Ma’ana

Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu [1]suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta.

[1] Wannan ãyã tanã nũna yadda wani ke ceton wani sabõda kusanci dõmin a ƙãra daukaka mai ceton. Sharaɗin ceton shĩ ne wanda ake ceton yanã da nãsa ĩmanin. Wanda jinginarsa ta halaka bãbu mai cetonsa. Zuriya ta haɗa uwãye da almajiran mãlami sãlihi. Suna shiga a cikin cetonsa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

At-Tur

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net