Qaaf 50:39
قفَٱصْبِرْ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ قَبْلَ طُلُوعِ ٱلشَّمْسِ وَقَبْلَ ٱلْغُرُوبِ
Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi[1] game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta.
[1] Tasbĩhi game da gõdewa Allah a gabãnin fitar rãnã, shi ne sallar asuba, na gabãnin ɓacewarta, shi ne sallar Azahar da La'asar. Daga dare kuwa, shĩ ne sallar Magariba da Isha'i. Bãyan sujada, shĩ ne sallõli na nafila kuma ma'anarsa a nan tasbĩhi da tahmĩdi da kabbarõri a bãyan sallõli farillai talãtin da uku kõwace, sa'annan a cika ɗari da addu'ar da aka ruwaito a nan.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net