Qaaf 50:14
قوَأَصْحَـٰبُ ٱلْأَيْكَةِ وَقَوْمُ تُبَّعٍ ۚ كُلٌّ كَذَّبَ ٱلرُّسُلَ فَحَقَّ وَعِيدِ
Da ma'abũta ƙunci [1]da mutãnen Tubba'u,[2] kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata.
[1] Ma'abũta ƙunci, mutãnen shu'aibu ne na farko. Bãyan an halaka su, sa'an nan ya tafi Madayana.
[2] Tubba'u, sarkin Himyar ne,a Yemen, yã musulunta amma mutãnensa suka ƙi bin sa ga addini, aka halaka su, shi kuma ya tsĩra. Shĩ ne sarki wanda ya sãɓãwa ƙã'ida; ya musulunta amma mabiyansa ba su musulunta ba.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net