Al-Maaida 5:87
المائدةيَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تُحَرِّمُوا۟ طَيِّبَـٰتِ مَآ أَحَلَّ ٱللَّهُ لَكُمْ وَلَا تَعْتَدُوٓا۟ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ ٱلْمُعْتَدِينَ
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku haramta abubuwa mãsu dãɗi da Allah Ya halatta muku, kuma kada ku ƙetare haddi. Lalle ne, Allah bã Ya son mãsu ƙetare haddi.[1]
[1] Haramta abin da Allah Ya halatta kõ kuwa halatta abin da Allah Ya haramta kãfirci ne, dõmin wanda ya ƙetare haddi da kansa, yã yi da'awar Ilãhiyya kõ Annabci, haka wanda ya bi shi a kan wannan abin, ya yi shirki da Allah, dõmin yã sãmi wani mai waɗansu dõkõki wanda bã Allah ba, kuma ya bi shi a kansu, ko kuwa ya bi wani mai da'awar annabci, bãyan Alƙur'ãni yã ce an rufe annabci daga Annabi Muhammadu, tsĩra da amincĩ su tabbata a gare shi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net