Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 5 · Aya ta 82

Al-Maaida 5:82

المائدة

لَتَجِدَنَّ أَشَدَّ ٱلنَّاسِ عَدَٰوَةً لِّلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱلْيَهُودَ وَٱلَّذِينَ أَشْرَكُوا۟ ۖ وَلَتَجِدَنَّ أَقْرَبَهُم مَّوَدَّةً لِّلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱلَّذِينَ قَالُوٓا۟ إِنَّا نَصَـٰرَىٰ ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّ مِنْهُمْ قِسِّيسِينَ وَرُهْبَانًا وَأَنَّهُمْ لَا يَسْتَكْبِرُونَ

Ma’ana

Lalle ne kana sãmun mafiya tsananin mutãne a adãwa ga waɗanda suka yi ĩmãni, Yahudu ne da waɗanda suka yi shirki. Kuma lalle ne kanã sãmun mafiya kusantarsu a sõyayya ga waɗanda suka yi ĩmãni su ne waɗanda suka ce: "Lalle mu ne Nasãra." Wancan kuwa sabõda akwai ¡issawa da ruhubãnãwa[1] daga cikinsu. Kuma lalle ne su, bã su yin girman kai.

[1] Ƙissĩsi shĩ ne lĩmãnin kiristãwa, ruhubãnanci shĩ ne mutum ya tsabbace daga mutãne dõmin ibãda, kuma ba ya yin aure. Baruhubãne guda, ruhubãnãwa jam'i.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Maaida

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net