Al-Maaida 5:72
المائدةلَقَدْ كَفَرَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓا۟ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلْمَسِيحُ ٱبْنُ مَرْيَمَ ۖ وَقَالَ ٱلْمَسِيحُ يَـٰبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ رَبِّى وَرَبَّكُمْ ۖ إِنَّهُۥ مَن يُشْرِكْ بِٱللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ ٱللَّهُ عَلَيْهِ ٱلْجَنَّةَ وَمَأْوَىٰهُ ٱلنَّارُ ۖ وَمَا لِلظَّـٰلِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ
Lalle ne haƙĩƙa waɗanda[1] suka ce: "Lalle ne Allah, shĩne Masĩhu, ɗan Maryama," sun kãfirta. Alhãli kuwa Masĩhu yã ce: "Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku bauta wa Allah Ubangijina, kuma Ubangijinku." Lalle ne shĩ, wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne, Allah Yã haramta masa Aljanna. Kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai.
[1] Su ne Ya'aƙũbiyya, Bãyan bayãni a kan aibõbin Yahũdu sai Ya shiga bayãni a kan aibõbin Nasãra.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net