Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 5 · Aya ta 64

Al-Maaida 5:64

المائدة

وَقَالَتِ ٱلْيَهُودُ يَدُ ٱللَّهِ مَغْلُولَةٌ ۚ غُلَّتْ أَيْدِيهِمْ وَلُعِنُوا۟ بِمَا قَالُوا۟ ۘ بَلْ يَدَاهُ مَبْسُوطَتَانِ يُنفِقُ كَيْفَ يَشَآءُ ۚ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرًا مِّنْهُم مَّآ أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ طُغْيَـٰنًا وَكُفْرًا ۚ وَأَلْقَيْنَا بَيْنَهُمُ ٱلْعَدَٰوَةَ وَٱلْبَغْضَآءَ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۚ كُلَّمَآ أَوْقَدُوا۟ نَارًا لِّلْحَرْبِ أَطْفَأَهَا ٱللَّهُ ۚ وَيَسْعَوْنَ فِى ٱلْأَرْضِ فَسَادًا ۚ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلْمُفْسِدِينَ

Ma’ana

Kuma Yahudu suka ce: "Hannun Allah abin yi wa ƙuƙumi ne.[1] " An sanya hannuwansu a cikin ƙuƙumi! Kuma an la'ane su sabõda abin da suka faɗa. Ã'a, hannuwanSa biyu shimfiɗaɗɗu ne, Yanã ciyarwa yadda Yake so. Kuma lalle ne abin da aka saukar zuwa gare ka yanã ƙãra wa mãsu yawa daga gare su, girman kai da kãfirci. Kuma Mun jefa a tsakãninsu, ƙiyayya da ƙeta, zuwa Rãnar ¡iyãma, kõ da yaushe suka hura wata wuta dõmin yãƙi, sai Allah Ya bice ta. Sunã aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna, alhãli kuwa Allah bã Ya son mãsu fasãdi.

[1] Suna nufin wai Allah marowaci ne.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Maaida

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net