Al-Maaida 5:60
المائدةقُلْ هَلْ أُنَبِّئُكُم بِشَرٍّ مِّن ذَٰلِكَ مَثُوبَةً عِندَ ٱللَّهِ ۚ مَن لَّعَنَهُ ٱللَّهُ وَغَضِبَ عَلَيْهِ وَجَعَلَ مِنْهُمُ ٱلْقِرَدَةَ وَٱلْخَنَازِيرَ وَعَبَدَ ٱلطَّـٰغُوتَ ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ شَرٌّ مَّكَانًا وَأَضَلُّ عَن سَوَآءِ ٱلسَّبِيلِ
Ka ce: "Shin, in gaya muku mafi sharri daga wannan, dõmin sakamako[1] daga wurin Allah? wanda Allah Ya la'ane shi kuma Ya yi fushi da shi, kuma Ya sanya daga gare su birai da aladai, kuma ya bauta wa ¦ãguta. Waɗannan ne mafiya sharrin wuri, kuma mafiya ɓata daga tsakar hanya."
[1] Kunã son in gaya muku ba dõmin ku bã ni wani sakamako ba, sai dõmin Allah Ya sãkã mini. Mutãnen da aka jũyar suka kõma birai da aladai kuma suka bauta wa wanin Allah, su ne mafi sharrin mutãne.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net