Al-Maaida 5:41
المائدةيَـٰٓأَيُّهَا ٱلرَّسُولُ لَا يَحْزُنكَ ٱلَّذِينَ يُسَـٰرِعُونَ فِى ٱلْكُفْرِ مِنَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا بِأَفْوَٰهِهِمْ وَلَمْ تُؤْمِن قُلُوبُهُمْ ۛ وَمِنَ ٱلَّذِينَ هَادُوا۟ ۛ سَمَّـٰعُونَ لِلْكَذِبِ سَمَّـٰعُونَ لِقَوْمٍ ءَاخَرِينَ لَمْ يَأْتُوكَ ۖ يُحَرِّفُونَ ٱلْكَلِمَ مِنۢ بَعْدِ مَوَاضِعِهِۦ ۖ يَقُولُونَ إِنْ أُوتِيتُمْ هَـٰذَا فَخُذُوهُ وَإِن لَّمْ تُؤْتَوْهُ فَٱحْذَرُوا۟ ۚ وَمَن يُرِدِ ٱللَّهُ فِتْنَتَهُۥ فَلَن تَمْلِكَ لَهُۥ مِنَ ٱللَّهِ شَيْـًٔا ۚ أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ لَمْ يُرِدِ ٱللَّهُ أَن يُطَهِّرَ قُلُوبَهُمْ ۚ لَهُمْ فِى ٱلدُّنْيَا خِزْىٌ ۖ وَلَهُمْ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ عَذَابٌ عَظِيمٌ
Yã kai Manzo! Kada waɗanda suke tseren gaugawa a cikin kãfirci su ɓãta maka rai, daga waɗanda suka ce: "Mun yi ĩmãni" da bãkunansu, alhãli zukatansu ba su yi ĩmãnin ba, kuma daga waɗanda suka tuba (watau Yahudu) mãsu yawan saurare ga wasu mutane na dabam waɗanda ba su je maka ba, sunã karkatar da zance daga bãyan wurarensa, sunã cewa: "Idan an bã ku wannan, to, ku karɓa, kuma idan ba a bã ku shĩ ba, to, ku yi sauna."Kuma wanda Allah Ya yi nufin fitinarsa, to bã zã ka mallaka masa kõme ba, daga Allah. Waɗannan ne waɗanda Allah bai yi nufin Ya tsarkake zukãtansu ba. Sunã da kunya a cikin duniya, kuma sunã da wata azãba mai girma a cikin ãhira.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net