Al-Maaida 5:35
المائدةيَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ وَٱبْتَغُوٓا۟ إِلَيْهِ ٱلْوَسِيلَةَ وَجَـٰهِدُوا۟ فِى سَبِيلِهِۦ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, kuma ku nemi tsari zuwa gare shi, kuma ku yi jihãdi[1] a cikin hanyarsa, tsammãninku, za ku ci nasara.
[1] Wasĩla ita ce dukkan aikin ibãda wanda zai kusantar da mutum zuwa ga Ubangijinsa, amma da sharaɗin an gina shi a kan taƙawa. Kuma taƙawa ita ce bin Allah kamar yadda Ya yi umurni a bi Shi, ta hanyar manzon Sa kawai. Jihãdi yana cikin taƙawa amma Yã kõma ambatonsa ne domin muhimmancinsa. Shi kuma iri biyu ne: ƙararmi, watau yãƙin abokan gãbã na bayyane, da babba, shi ne yãƙin abokan gãbã na ɓoye, watau rai da shaiɗan. Wanda maƙiyinsa na bayyane ya kashe shi yã mutu shahĩdi, wanda maƙiyinsa na ɓoye ya kashe shĩ ya mutu fãsiƙi ko kãfiri watau shaƙiyyi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net