Al-Maaida 5:32
المائدةمِنْ أَجْلِ ذَٰلِكَ كَتَبْنَا عَلَىٰ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ أَنَّهُۥ مَن قَتَلَ نَفْسًۢا بِغَيْرِ نَفْسٍ أَوْ فَسَادٍ فِى ٱلْأَرْضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ ٱلنَّاسَ جَمِيعًا وَمَنْ أَحْيَاهَا فَكَأَنَّمَآ أَحْيَا ٱلنَّاسَ جَمِيعًا ۚ وَلَقَدْ جَآءَتْهُمْ رُسُلُنَا بِٱلْبَيِّنَـٰتِ ثُمَّ إِنَّ كَثِيرًا مِّنْهُم بَعْدَ ذَٰلِكَ فِى ٱلْأَرْضِ لَمُسْرِفُونَ
Daga sababin wannan,[1] Muka rubuta a kan Banĩ lsrã'ĩla cewa, lalle ne wanda ya kashe rai bã da wani rai ba, ko ɓarna a cikin ƙasa, to kamar yã kashe mutãne duka ne, kuma wanda ya rãya rai, to, kamar yã rãyar da mutãne ne gabã ɗaya. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Manzannin Mu sun je musu da hujjõji bayyanannu, sa'an nan kuma lalle ne, mãsu yawa daga gare su, a bãyan wannan, haƙĩƙa, mãsuɓarna ne a cikin ƙasa.
[1] Aikata ƙaramin laifi yana sabbaba babban laifi har ɓarna mai yawa ta wãtsu a cikin ƙasa.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net