Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 5 · Aya ta 27

Al-Maaida 5:27

المائدة

وَٱتْلُ عَلَيْهِمْ نَبَأَ ٱبْنَىْ ءَادَمَ بِٱلْحَقِّ إِذْ قَرَّبَا قُرْبَانًا فَتُقُبِّلَ مِنْ أَحَدِهِمَا وَلَمْ يُتَقَبَّلْ مِنَ ٱلْـَٔاخَرِ قَالَ لَأَقْتُلَنَّكَ ۖ قَالَ إِنَّمَا يَتَقَبَّلُ ٱللَّهُ مِنَ ٱلْمُتَّقِينَ

Ma’ana

Kuma karantã musu[1] lãbãrin ɗiya biyu[2] na Ãdamu, da gaskiya, a lõkacin da suka bãyar da baiko, sai aka karɓa daga ɗayansu kuma ba a karɓa daga ɗayan ba, ya ce: "Lalle ne zan kashe ka." (¦ayan kuma) ya ce: "Abin sani dai, Allah Yana karɓã daga mãsu taƙawa ne."

[1] Ƙuraishawa ko kuwa al'ummarka.
[2] Ɗiyan Ãdamu, biyu, Ƙãbĩla da Hãbĩla. Asalin maganar kamar yadda aka ruwaito, mãtar Ãdamu, Hauwa'u, tana haifuwar namiji da mace a kowane ciki, wajen aure sai a shirɓata dõmin bãbu wasu mutãne sai su. Sai Ƙabĩla ya ƙi yarda a bai wa Hãbĩla 'yar'uwarsa, har Ãdam ya sanya su yin baiko da abin sana'arsu. Ƙãbĩla manõmi ne, ya bãyar da munãna daga kãyan nõmansa, shi kuma Hãbĩla ya bãyar da rãgo mai kyau dõmin sana'arsa kiwo ne. Sai wuta ta sauko ta ɗauki rãgon Hãbĩla, alãmar karɓa. Wannan kuwa ya ɗauki Ƙãbĩla ga tunãnin kashe shi. Laifi guda yana sabbaba wasu laifuka mãsu yawa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Maaida

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net