Al-Maaida 5:11
المائدةيَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ ٱذْكُرُوا۟ نِعْمَتَ ٱللَّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ هَمَّ قَوْمٌ أَن يَبْسُطُوٓا۟ إِلَيْكُمْ أَيْدِيَهُمْ فَكَفَّ أَيْدِيَهُمْ عَنكُمْ ۖ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ۚ وَعَلَى ٱللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ ٱلْمُؤْمِنُونَ
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da wasu mutãne suka yi niyyar su shimfiɗa hannuwansu zuwa gare ku[1] sai Ya kange hannuwansu daga gare ku, kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma sai muminai su dogara ga Allah kawai.
[1] Wannan kiyãyewa ya auku a wurãre da yawa tun Musulmi suna da rauni kuma kãfirai suna da ƙarfi, kuma suna son su kashe Musulmi da Musulunci. Allah Ya tsare su. Saboda haka yanzu da Musulmi suka yi ƙarfi da ƙarfin Allah, yã wajaba a kansu su godewa Allah da taƙawa. Watau su riƙe alkawarin Allah, su yi abin da Ya aza musu gwargwadon hãli.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net