Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 5 · Aya ta 109

Al-Maaida 5:109

المائدة

يَوْمَ يَجْمَعُ ٱللَّهُ ٱلرُّسُلَ فَيَقُولُ مَاذَآ أُجِبْتُمْ ۖ قَالُوا۟ لَا عِلْمَ لَنَآ ۖ إِنَّكَ أَنتَ عَلَّـٰمُ ٱلْغُيُوبِ

Ma’ana

A ranar da Allah Yake tãra manzanni sa'an nan Ya ce: "Mene ne aka karɓa muku?" (zã) su ce: "Bãbu ilmi a gare mu. Lalle ne Kai, Kai ne Masanin abubuwan fake."[1]

[1] A nan hukunce-hukuncen alkawurra suka ƙãre a wannan sura daga ãyã ta sama da wannan. Kuma da wannan ãyã ta l09 Allah Yanã yi mana hikãyar abin da zai auku a Lãhira da bincinken Sa ga tsare alkawari, kõ rashin tsarewa. Ya fãra da Annabãwan Sa. Ya aiko, da ƙarin bãyani a kan irin muhãwarar da zã ta shiga a tsakãnin Sa da Annabãwa.Yã yi misãli da Ĩsã dõmin mutanensa nã nan a cikin wannan al'umma, anã kiran su zuwa ga musulunci, kuma domin shine Annabi na ƙarshen da ba a manta abubuwan da mutanensa suka yi ba a gabanin ɗauke shi ɗin.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Maaida

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net