Al-Hujuraat 49:1
الحجراتيَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تُقَدِّمُوا۟ بَيْنَ يَدَىِ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ۖ وَٱتَّقُوا۟ ٱللَّهَ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٌ
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku gabãta (da kõme) gaba ga Allah da Manzon Sa.[1] Kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai ji ne, Masani.
[1] Wannan yã nũna mana cewa bã yã halatta ga Musulmi ya yi wani aiki ko ya faɗi wata magana sai yã san hukuncin Allah a cikinsu. Kuma kada ya ƙãra wãyõnsa a kan abinda Allah Yã ce, kuma kada ya rage idan yanã da ĩkon cikãwa. Dukan wannan yakan ja Musulmi ga ɓãcin ayyukansa, watau ya yi ridda daga Musulunci.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net