Al-Fath 48:24
الفتحوَهُوَ ٱلَّذِى كَفَّ أَيْدِيَهُمْ عَنكُمْ وَأَيْدِيَكُمْ عَنْهُم بِبَطْنِ مَكَّةَ مِنۢ بَعْدِ أَنْ أَظْفَرَكُمْ عَلَيْهِمْ ۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرًا
Kuma Shĩ ne Ya kange hannayensu [1]daga gare ku, kuma da hannayenku daga gare su, a cikin Makka, bãyan Ya rinjãyar da ku a kansu. Kuma Allah Ya kasance Mai gani ga abin da kuke aikatãwa.
[1] Waɗansu Ƙuraishawa ne, sũ tamãnin, suka kewaye Musulmi a Hudaibiyya, da niyyar yaudara, sai aka kãme su, su duka, aka kai su ga Annabi, shi kuma ya yãfe musu, a bãyan ya nũna musu rinjãya. Wannan shĩ ne ya sabbaba yin sulhu.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net