Al-Fath 48:15
الفتحسَيَقُولُ ٱلْمُخَلَّفُونَ إِذَا ٱنطَلَقْتُمْ إِلَىٰ مَغَانِمَ لِتَأْخُذُوهَا ذَرُونَا نَتَّبِعْكُمْ ۖ يُرِيدُونَ أَن يُبَدِّلُوا۟ كَلَـٰمَ ٱللَّهِ ۚ قُل لَّن تَتَّبِعُونَا كَذَٰلِكُمْ قَالَ ٱللَّهُ مِن قَبْلُ ۖ فَسَيَقُولُونَ بَلْ تَحْسُدُونَنَا ۚ بَلْ كَانُوا۟ لَا يَفْقَهُونَ إِلَّا قَلِيلًا
Waɗanda aka bari zã su ce idan kun tafi zuwa ga waɗansu ganĩmõmi[1] dõmin ku karɓo su, "Ku bar mu, mu bĩ ku." Sunã son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: "Bã zã ku bĩ mu ba. Kamar wannan ne Allah Ya ce, a gabãnin haka." Sa'an nan zã su ce: "Ã'a, kunã dai hãssadar mu ne." Ã'a, sun kasance bã su fahimtar (abũbuwa) sai kaɗan.
[1] A bãyan sulhun Hudaibiyya Allah Ya yi wa Annabi alkawarin zai buɗe masa Haibara ya sãmi ganĩma mai yawa, amma kuma kada ya bari ƙauyãwan da aka nema su fita zuwa Makka, suka ƙi su fita tãre da shi.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net