Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 47 · Aya ta 36

Muhammad 47:36

محمد

إِنَّمَا ٱلْحَيَوٰةُ ٱلدُّنْيَا لَعِبٌ وَلَهْوٌ ۚ وَإِن تُؤْمِنُوا۟ وَتَتَّقُوا۟ يُؤْتِكُمْ أُجُورَكُمْ وَلَا يَسْـَٔلْكُمْ أَمْوَٰلَكُمْ

Ma’ana

Rãyuwar dũniya, wãsã da abin shagala kawai[1] ce, kuma idan kun yi ĩmãni, kuma kun yi taƙawa, Allah zai kãwo muku ijarõrinku, kuma bã zai tambaye ku dũkiyarku ba.

[1] Wãsã, shi ne dukan aiki wanda aka yi bã da nufin wata fa'ida ta addini ba, watau anã yin sa ne dõmin a sãmi abin aikatãwa a ɓãta lõkaci. Dukan ayyukan da mutum ya yi da nufin rãyuwar dũniya kawai, to, ya zama wãsã kõ dã cin abinci ne da karãtu. Kuma duk abin da mutum ya yi da niyyar bin umurnin Allah, wãjibi to ya zama aikin Lãhira kõ da cin abinci ne da jima'insa da matarsa, kamar yadda yake a cikin Hadĩsin Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Muhammad

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net