Al-Ahqaf 46:29
الأحقافوَإِذْ صَرَفْنَآ إِلَيْكَ نَفَرًا مِّنَ ٱلْجِنِّ يَسْتَمِعُونَ ٱلْقُرْءَانَ فَلَمَّا حَضَرُوهُ قَالُوٓا۟ أَنصِتُوا۟ ۖ فَلَمَّا قُضِىَ وَلَّوْا۟ إِلَىٰ قَوْمِهِم مُّنذِرِينَ
Kuma a lõkcin da Muka jũya waɗansu jama'a na aljamiu[1] zuwa gare ka sunã saurãren Alƙur'ãni. To, alõkacin da suka halarce shi suka ce: "Ku yi shiru." Sa'an nan da aka ƙãre, suka jũya zuwa ga jama'arsu sunã mãsu gargaɗi.
[1] Wannan yã nũna cewa a cikin aljannu akwai Musulmi da masu gargaɗi, kuma idan mutum ya yi gargaɗi, dõmin Allah, Allah zai taimake shi da mãsu saurãra masa, kõ da daga waɗansu jinsin da ba nãsa ba. Kuma zama a cikin wani addinin Allah da ya shige, ba ya isa ga wanda bai shiga addinin Musulunci ba, a bãyan bayyanar Musulunci.
Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com
Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net