Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 46 · Aya ta 21

Al-Ahqaf 46:21

الأحقاف

وَٱذْكُرْ أَخَا عَادٍ إِذْ أَنذَرَ قَوْمَهُۥ بِٱلْأَحْقَافِ وَقَدْ خَلَتِ ٱلنُّذُرُ مِنۢ بَيْنِ يَدَيْهِ وَمِنْ خَلْفِهِۦٓ أَلَّا تَعْبُدُوٓا۟ إِلَّا ٱللَّهَ إِنِّىٓ أَخَافُ عَلَيْكُمْ عَذَابَ يَوْمٍ عَظِيمٍ

Ma’ana

Kuma ka ambaci ɗan'uwan[1] Ãdãwa a lõkacin da ya yi gargaɗi ga mutãnensa, a Tuddan Rairayi, alhãli kuwa waɗansu mãsu gargaɗi sun shũɗe agaba gare shi da bãya gare shi (da cẽwa) "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ inã tsõrata muku azãbar yini mai girma."

[1] Ya ambaci hũdu da mutãnensa Ãdãwa da misãlin waɗansu mãsu garagaɗi daga Annabãwan da suka shũɗe da kuma mutãnensu da yadda aka halaka su daga inda suke zaton rahama ta Je musu. Haka ne hukuncin. Dukan wanda aka yi wa gargaɗi da bin umurnin Allah, idan ya ƙi bi, sa'an nan ya bi son zũciyarsa, Allah zai Kãwo masa azãba daga inda yake zaton alheri ga kansa.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Ahqaf

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net