Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 45 · Aya ta 26

Al-Jaathiya 45:26

الجاثية

قُلِ ٱللَّهُ يُحْيِيكُمْ ثُمَّ يُمِيتُكُمْ ثُمَّ يَجْمَعُكُمْ إِلَىٰ يَوْمِ ٱلْقِيَـٰمَةِ لَا رَيْبَ فِيهِ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ

Ma’ana

Ka ce: "Allah ne ke rãyar[1] da ku kuma Shĩ ne ke matarda ku, sa'an nan Ya tãra ku zuwa ga Rãnar ¡iyãma, bãbu shakka a gare ta, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba."

[1] Wãtau ba kũ ne ke rãyuwa da kanku ba, sai an rãyar da ku, haka ne ga mutuwa, bã ku ne ke mutuwa da kanku ba, sai an matar da ku, kuma Allah Shi Ɗaya ke iya rãyarwa ko matarwa. To, yãya ne zã ku ƙi bin sharĩ'ar da Ya umurce ku da binta?.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Jaathiya

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net