Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 42 · Aya ta 51

Ash-Shura 42:51

الشورى

وَمَا كَانَ لِبَشَرٍ أَن يُكَلِّمَهُ ٱللَّهُ إِلَّا وَحْيًا أَوْ مِن وَرَآئِ حِجَابٍ أَوْ يُرْسِلَ رَسُولًا فَيُوحِىَ بِإِذْنِهِۦ مَا يَشَآءُ ۚ إِنَّهُۥ عَلِىٌّ حَكِيمٌ

Ma’ana

Kuma bã ya kasancẽwa ga wani mutum Allah Ya yi masa magana[1] fãce da wahayi, kõ daga bãyan wani shãmaki, kõ Ya aika wani Manzo, sa'an nan Ya yi wahayi, da izninsa ga abin da Yake so. Lalle Shĩ, Maɗaukaki ne Mai hikima.

[1] Annabãwa a lõkacin da Allah Ya yi musu magana ba su gan shi ba, sai dai sun ji maganarsa kamar yadda Musã ya ji, kõ kuma da wãsiɗar malã'ika kamar sauran Annabãwa, kõ kuwa da ilhama watau ya san hukunci ba da magana kõ wani wãsiɗar malã'ika ba. Ilhãmar Annabãwa da mafarkinsu gaskiya ne. Ilhãma da mafarkin sauran mutãne bã ya zama hujja sai idan yã dãce da shari'a, sai a yi aiki da shi a kan shari'a bã a kan mafarkin ko ilhãmar ba.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Ash-Shura

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net