Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Sura ta 40 · Aya ta 83

Al-Ghaafir 40:83

غافر

فَلَمَّا جَآءَتْهُمْ رُسُلُهُم بِٱلْبَيِّنَـٰتِ فَرِحُوا۟ بِمَا عِندَهُم مِّنَ ٱلْعِلْمِ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ

Ma’ana

A lõkacin da Manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, suka yi farin ciki da abin da ke wurinsu na ilmi[1] kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi ya wajaba a kansu.

[1] Ilmin dũniya na sanã'õ'i ya zõ ne daga Annabãwa kamar na ibãdu. Nũhu ya fãra sassaƙar jirgin ruwa da wahayi daga Allah, Zulƙarnaini ya fãra haɗa baƙin ƙarfe da gaci dõmin hana tsãtsa, Yũsufu ya fãra barin hatsi a cikin sõshiya dõmin hana ƙwãri. Dãwũda ya fãra sanã'ar sulke. Ãdam ya fara rubũtu, Idirĩsu ya fara yin alƙalami. ĩsã ya fãra warkar da majinyata, Alƙur' ãni ya nũna anã iya tãshi sama da jirgin sama. Shu'aibu shi ya nũna kasuwanci, da sauransu.

Ma’ana: Hausa Translation - Abu Bakr Jumi. Translated by Abu Bakr Mahmoud Jumi, developed under the supervision of the Rowwad Translation Center. The original translation is available for the purpose of expressing opinion, evaluation, and continuous development. Sigar 1.2.2, 2025-06-26. QuranEnc.com

Al-Ghaafir

Larabcin rubutun Tanzil ne, ba tare da canji ba. Ma’anonin bugun mawallafansu ne, ba tare da canji ba; masu bitar Sabīl kansu ba su duba su ba tukuna. Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil, sigar 1.1. Tushe: tanzil.net